About To Goni Bukar

Goni Bukar Memorial Islamic Academy makaranta ce da aka ginata domin karantar da al'umma ilimin Qur'an da sauran littatafai na addinin musulunci. GONI BUKAR sunane na ma haifin wanda ya gina wannan makaranta (ALHAJI USMAN) domin Allah ya kai lada har zuwa makwancinsu. Allah yasa albarka a rayuwar su ya kuma saka musu da aljannatul firdaus. Anfara karatu a wannan makaranta da ɗalibai 12 a shekarar 2016. Director na wannan makaranta shine DR. BASHIR MUHAMMAD ALI Allah ya sawa rayuwa albarka.

More About Goni Bukar School

Goni Bukar Memorial Islamic Academy makaranta ce da aka ginata domin karantar da al'umma ilimin Qur'an da sauran littatafai na addinin musulunci. GONI BUKAR sunane na ma haifin wanda ya gina wannan makaranta (ALHAJI USMAN) domin Allah ya kai lada har zuwa makwancinsu. Allah yasa albarka a rayuwar su ya kuma saka musu da aljannatul firdaus. Anfara karatu a wannan makaranta da ɗalibai 12 a shekarar 2016. Director na wannan makaranta shine DR. BASHIR MUHAMMAD ALI Allah ya sawa rayuwa albarka.

Littattafai Da Ake Karantarwa Sune:

  1. Qur'an
  2. Hadith
  3. Tauhid
  4. Fiqhu
  5. Azkar
  6. Huruf
  7. Luggatul Arabia
  8. English (Safe)
  9. Mathematics (Safe)
  10. Basic Science (Safe)
  11. Social Studies (Safe)

Makaranta tana fara karantar da Qur'an da Huruf da Azkar ma yaran Rauda domin sune ginshikin duk wani karatu, yayin da aka fara karantar da su Qur'an zai buɗemu musu ƙwa-ƙwalwa sannan Huruf kuma zai taimaka musu wajen iya haɗa baƙin larabci Azkar kuma zai taimaka musu wajen sani addu'o'i na yau da kullum wannan sune dalilan da yasa muke fara karantar da su littatafai kaɗan domin su samu background kuma shi yaro yana da kyau afara masa da karatu kaɗan kafin ƙwa-ƙwalwansa ya buɗu, yayinda sukafara fahimtar wannan idan suka shiga Aji ɗaya sai afara ƙara musu sauran littatafai da kaɗan kaɗan har zuwa asa musu dukkan littafan gaba ɗaya. Dayamma Bama karantar da boko saboda mafi yauwa suna boko saide Qur'an da sauran littatafai na addinin musulunci, na safe kuma muna samusu boko ne saboda su san wasu abubuwa a karatun zamani, sannan shima munafarawane da English da Mathematics saboda sune Basics dagabaya sai musa musu Basic Science da Social Studies. Muna buɗe makaranta daga 7:00am har zuwa 6:00pm kuma munafara karatu da safe 7:30am mutashi 12:20pm da yamma kuma 2:00pm har zuwa 5:20pm. Wanda yake na safe zaizo daga 7:00am har zuwa 12:20pm yatafi gida wanda yake yamma zaizo daga 2:00pm har zuwa 5:20pm sai atashi, wanda yake wuni kuma tun karfe 7:00am idan yazo bazai koma gidaba sai karfe 5:20pm idan antashi gaba ɗaya. Makaranta tana bada alfarma wanda yake na yamma zai iya zuwa ranan Lahadi ya wuni domin ya ƙaru da karatukan safe da ake yi musamman ma muraja'a, haka zalika idan amda putun boko muna alfarma da ɗalibai na yamma suna zuwa da safe har putunsu yakere domin suna ƙara muraja'a. A 2021 makaranta ta kawo wani tsari na muraja'a da kaɓan haddan baya ranan Lahadi da safe ma ɗaliban yamma wanda karatunsu yayi nisa dan suzo suna ƙara samun daman muraja'a. Ana fara muraja'anne ƙarfe 6:00am zuwa 8:00am hour 2 za'afara tun daga farkon karatu (Baqara) har inda Allah ya sa aka tsaya, sai sutafi gida suyi break su dawo 9:00am sai a karɓa haddansu na baya domin su dunga gyara karatunsu na baya dan kar yanazubewa dayamma kuma sai subada haddan sabon karatunsu. Kamar yanda mukasi cewa wannan makaranta ce haddan Alqur'ani mai girma shiyasa muke ƙara ƙarfi akan haddan Alqur'ani kuma dan musamu muga cewa mun karantar da ɗalibai ingan taccen karatu.

Manufofi Da Abunda Muke So Mucimma

Manu farmu shine mukarantar da ɗalibai ingantaccen karatu da zai taimaka musu wajen yin ibadunsu da kuma karantar da sauran al'ummar Musulmi domin idan ba'a karantar da ɗalibai karatu mai inganci ba babu yanda zasu je su suka rantar me kyauba kuma hakan zai sa adunga yawo gurɓataccen karatu.

Abunda muke so mucimma shine muga cewa ansamu makaranta addini da hakane musulunci zai cigaba da ya ɗuwa sannan kuma da samun falala na wanda ya koyi Alqur'ani kuma ya karantar da shi kamar yanda Annabi Muhammad (S.A.W) yace: خير كم من تعلم القرآن وعلمه Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce mafi alkhairin cikin ku shine wanda ya koyi Alqur'ani kuma ya koyar da shi.

Goni Bukat Memorial Islamic Academy (Staff)

School Director

Dr. Bashir Muhammad Ali

Senior Master/ Social Master

Mustapha Ali

Financial Secretary/Program Master

Muhammad Nuhu

Addmission/Exam and Record

Ismail Junaidu

Works officer/Labour Master

Bashir Muhammad

Assitant Program Master

Muhammad Msua

Assitant Social Master

Muhammad Ibrahim

Class Teacher

Ibrahim Musa

Awarting Position

Awarting


Full Address